HausaNewsPolitics

Ziyarar Kungiyar ‘The Dawn for Good Governance Initiative’

Dalhat Hamid Bello

Kungiyar Samar Da Shugabanci na Gari Tsaknin Al’umma, wato Dawn for Good Governance Initiative , ta halarci shirin kai tsaye bna Radio LYB don tattaunawa kan manufofi, tsare-tsare da ayyukan da kungiya ta sa a gaba a kokarin samar da shugabanci na kwarai cikin al’umma, bisa tafarki na gudanar da siyasa karkashin tsarin dimokradiyya.
A cikin shirin na ‘Leka Gidan Kowa’, shugaban kunigiyar Imam Muhammad ibn Ali, tare da Imrana Ahmad, wani jigo a harkar kungiyar sun bayyana muhimmancin daukan matakai na gaggawa don dawo da hankalin al’umma kan zabo mutane na gari kan madafun mulki da wakilci a duk lokacin zabe tsakanin ‘yan takara masu neman shugabanci.
A cewar shugabannin kungiyar Dawn for Good Governance, wannan aiki ne da ya rataya kan dukkan bangarorin al’umma, musamman shugabanni, malaman addini, masu fada a ji, kana da sauran daidaiku da kowa ke da hakki ya ba da gudumawa don fadakar da al’umma kan wannan muhimmin aiki na samar da shugabanci na kwarai.
Kungiyar ta ce ta sha damara, kuma ta yi azama kan wannan aiki, kuma a yanzu tafiya ta yi nisa don tabbatar da wannan muradi da karfafa manufa. Za a iya sauraron maimaita wannan shirin da karfe 10:00 na dare a sashen wasa shirye-shirye cikin sauti na Radio LYB, kazalika da karfe 7:00 na safe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button