News

Tinubu zai fuskanci babban ƙalubale a Arewa

Bashir Ahmad

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Najeriya (ACF) ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai fuskanci babban ƙalubale wajen samun goyon bayan al’ummar yankin Arewa a babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Ƙungiyar ta danganta wannan gargaɗi da zargin cewa an mayar da yankin Arewa tamkar saniyar ware, baya ga matsanancin matsin rayuwa da mazauna yankin ke fama da shi. A cewar ƙungiyar, ƙorafe-ƙorafen da ake yi wa gwamnati ba su tsaya a Arewa kaɗai ba, domin kuwa ‘yan Najeriya a sassa daban-daban na ƙasar na fuskantar tsadar rayuwa, talauci, da kuma matsalar rashin tsaro.

“Mutane ba su ga maslaha ba” — Farfesa Tukur Baba

Da yake ƙarin haske kan matsayar ƙungiyar, Sakataren Yaɗa Labarai na ACF, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya nuna damuwa kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi a cikin ‘yan shekarun nan, inda ya yi watsi da hujjar gwamnati cewa sauye-sauyen da ta kawo na ɗan lokaci ne domin jawo masu zuba jari.

“Wannan kalamu ne da gwamnati ke yi. Mu kuma muna magana ne kan abin da mutane suke ji a ƙasa. Gaskiya mutane ba su ga maslaha ba; yanzu akwai wanda zai ce ya yabi gwamnati?” in ji Farfesa Baba.

Ya kuma yi fatali da iƙirarin da magoya bayan gwamnati ke yi cewa suna da miliyoyin masoya a Arewa, yana mai cewa abubuwan da ke faruwa a wuraren yaƙin neman zaɓe suna tayar da hankali. Ya ja hankalin al’umma da su guji tashin hankali kamar jife-jife, doke-doke, ƙone-ƙone, ko kashe-kashe, yana mai tunatar da su cewa ko bayan zaɓe akwai ƙasa, don haka hanyar da ta dace ita ce neman katin zaɓe.

Martanin Fadar Shugaban Ƙasa

Da yake mayar da martani kan kalaman na ACF, ɗaya daga cikin masu taimaka wa Shugaban Najeriya, Abdul’aziz Abdul’aziz, ya amince cewa akwai ƙalubale, amma ya ce an fara ganin haske sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Tinubu ta ɓullo da su.

Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ɗora ƙasar a kan turbar ci gaba, inda ya yi nuni da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin ke gudanarwa. “Duk wanda ke tafiya ta kilomita 400 zuwa 700 a Najeriya, ba inda zai je ba tare da ya ga sabon aiki da ake yi ba, tun daga makarantu zuwa manyan hanyoyi,” in ji shi.

Dangane da matsalar tsaro da talauci a Arewa da tsakiyar Najeriya, Abdul’aziz ya jaddada cewa gwamnati ta tura jami’an tsaro yankin kuma ana ci gaba da kai hare-hare a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma. Ya ƙara da cewa a halin yanzu ana zuwa kasuwanni da gonaki a wurare da dama da a baya ba su shiguwa, yayin da gwamnati ke ci gaba da ɗaukar ma’aikata da ɓullo da shirye-shiryen da za su kawo wa talaka sauƙi.

Wannan sa-in-sa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke ƙara zafafa shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, yayin da masana tsaro da tattalin arziƙi ke ci gaba da tsokaci kan halin da ƙasar ke ciki.

Back to top button