Uncategorized

Mutane Huɗu Sun Rasa Rayukansu, Biyar Sun Jikkata a Rikicin Garin Gurjiya a Jihar Jigawa

Isah Yakubu Isah

Mutane huɗu ne ake zargin sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyar ke kwance a asibiti suna karɓar magani sakamakon wani rikici da ƙone-ƙone da ya barke a garin Gurjiya da maƙwabtan ƙauyukansa da ke Jihar Jigawa.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Adam Shiisu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan wasu mahara sun far wa garin Gurjiya, inda suka fara ƙona bukkokin mazauna garin kafin su far wa mutane.

A cewarsa, a wannan hari na farko, mutum ɗaya ya rasa ransa nan take, yayin da aka jikkata mutane kusan biyar zuwa shida, inda daga bisani ɗaya daga cikin waɗanda suka jikkatan ya ce ga garinku nan a asibiti.

SP Shiisu ya ƙara da cewa ganin irin ɓarnar da aka tafka musu da kuma jikkata al’ummarsu, mazauna garin sun yi gangami zuwa maƙwabtan ƙauyukan da ake zaton na makiyaya ne domin ɗaukar fansa. A wannan harin ramuwar gayya, su ma sun ƙona bukkoki tare da kashe mutane biyu da jikkata wasu biyu, lamarin da ya kawo adadin waɗanda suka mutu zuwa huɗu.

Da yake magana kan matakan da jami’an tsaro suka ɗauka, kakakin ‘yan sandan ya ce da samun labarin faruwar lamarin, rundunar ‘yan sanda ta haɗa kai da jami’an haɗakar tsaro ta Operation Salama—wadda ta ƙunshi ‘yan sanda, sojoji, da jami’an tsaron farin kaya (Civil Defence)—tare da rundunar musamman ta yaƙi da manyan laifuka da ke ƙarƙashin shiyyar Dutse (Dutse Area Command), inda suka isa yankin domin kwantar da tarzomar.

Game da ko an kama wasu da ake zargi da hannu a rikicin, SP Lawan Adam Shiisu ya bayyana cewa har yanzu ba a kai ga yin kame ba. Ya jaddada cewa babban abin da jami’an tsaro suka sanya a gaba a halin yanzu shi ne tabbatar da an dawo da kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin.

Back to top button