
Garba Adamu GwanGwanGwan
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da daukar sabbin ma’aikata a dukkanin ma’aikatun gwamnati da hukumominta a shekarar 2027 mai zuwa.
Wannan na kunshe ne cikin wata takarda da ta fito daga Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, mai dauke da sa hannun Ishiyaku Musa Muhammed, Babban Sakatare mai kula da sashen Ayyuka da Tsare-tsare a ofishin.
An aike da takardar zuwa ga Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Sakataren Gwamnatin Tarayya, ministoci, manyan sakatarorin ma’aikatun tarayya, shugabannin hukumomin tsaro, da sauran shugabannin ma’aikatun gwamnati.
A cikin sabuwar sanarwar, wadda aka fitar a ranar 9 ga Nuwamba, 2026, an umurci dukkanin ma’aikatun gwamnati da su dakatar da daukar sabbin ma’aikata a shekarar 2027, har sai an tabbatar da sahihancin bukatar daukar ma’aikatan da kuma hanyoyin da za a bi wajen biyan hakkokinsu.
Saboda haka, an gargadi ma’aikatun gwamnati da hukumominsu da su guji kara yawan ma’aikatansu a shekarar 2027, matukar ba a samu amincewar da ta dace ba.
Bugu da kari, duk wata hukuma ko ma’aikatar gwamnati da ta ga wajabcin daukar sabbin ma’aikata, dole ne ta nemi izini da amincewa daga hukumomin da abin ya shafa kafin ta fara daukar ma’aikatan.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin inganta ayyukan gwamnati, da kuma tabbatar da cewa an tanadi isassun kudaden da za a biya dukkan ma’aikata hakkokinsu a cikin shekarar 2027.
Wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke shirin tunkarar babban zaben shekarar 2027. Haka kuma, ana iya kallon matakin a matsayin mai tsaurin gaske, to sai dai kuma masu sharhi akan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa shugaba Tinubu yayi kaurin suna wajen daukan matakai masu tsauri kamar yadda a shekaran 2023 ya cire tallafin man fetur, da wannan ne ma sharhantan suke cewa shawara ta rage ma yan Najeriya wajen zaban wanda zai iya hanasu aikin gwamnati.

