News

Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara ɗaya da rasuwa yau Juma’a

Bashir Ahmad

A yau Juma’a 27 ga Nuwamban 2026, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekara ɗaya da rasuwa.

Fitaccen malamin ya rasu ne ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025.

Shehin malamin ya rasu ne a asibitin sojojin sama da ke jihar Bauchi bayan gajeriyar jinya.

Ya kuma rasu yana da shekaru 98 a duniya.

Shiekh Dahiru Usman Bauchi babban malamin darikar Tijjaniyya ne da ake ji da shi a nahiyar Afirka, sannan malami ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga koyar da al’kur’ani, littafin Musulmi mafi girma.

Shehin malamin na ɗaya daga cikin malamai a Najeriya da suke sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa addinin Musulunci hidima.

Back to top button