Uncategorized

KANO: ‘Yan Daba Sun Far Wa Ayarin Kamfen Din Kwankwaso Da Gwarzo A Bichi

Abdulrahman Bala Katsinawa

Wasu da ake zargin ƴan daba ne sun far wa ayarin motocin kamfen ɗin tsohon gwamnan jihar Kano, kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar a Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, a lokacin wata ziyarar yaƙin neman zaɓe a ƙaramar hukumar Bichi ta jihar.

Kakakin ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar NDC, Kwamared Ibrahim Garba Shu’aibu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa tawagar kamfen ɗin ta samu nasarar ziyartar ƙananan hukumomin Tofa, Rimingado, Kabo, Gwarzo, Shanono da kuma Bagwai ba tare da wata tsangwama ba.

A cewarsa, tawagar ta samu rahoton cewa wasu mutane da ke adawa da gangamin siyasar sun tare hanyarsu ta zuwa Bichi.

Ya ce da isarsu Bichi, tawagar ta lura da alamun jifa da duwatsu kafin su wuce sakatariyar ƙaramar hukumar, inda wasu fusatattun matasa ɗauke da makamai suka ɓullo tare da far wa ayarin motocin.

Shu’aibu ya yi zargin cewa maharan sun ji wa wasu mambobin tawagar kamfen ɗin rauni, sannan suka lalata motoci da dama.

Ya ce da idonsa ya ga an farfasa motoci kusan bakwai a yayin wannan hari.

Rundunar ƴan sanda ba ta ce komai ba dangane da lamarin har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Back to top button