Aikin Sadarwa: Kwararre Ya Gargadi Masu Yada Labarai Kan Cin Zarafi da Kalaman Batanci

Isah Yakubu Isah
Wani kwararre a fannin sadarwa da hulda da jama’a, Kwamred Sabo Muhammad, ya yi kira ga marubuta, masu magana a kafafen yada labarai, da masu amfani da shafukan sada zumunta da su guji kalaman batanci, kazafi, da cin zarafin jama’a yayin isar da sakonni.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kwamred Sabo wanda ya taba rike mukamai a jami’o’i, gwamnati, da kungiyoyin kwararru tare da koyar da fannin sadarwa a manyan cibiyoyin ilimi, ya bayyana cewa aikin sadarwa da hulda da jama’a yana da tsari da ka’idoji wadanda suka haramta taba mutunci, kima, ko darajar dan’adam, komai kankantarsa.
Ya jaddada cewa sana’ar ta haramta yin kazafi, amfani da kalaman batsa, ko kiran sunan mutum kai tsaye ba tare da kwararan hujjoji ba. A cewarsa, mayar da martani cikin tsaftatattun kalamai da amfani da hikima wajen isar da sako ne ke kara daga darajar mai isar da sakon a idon al’umma.
Kwararren ya kuma ja hankali kan hadarin da ke tattare da rashin yin nazari kafin furta magana, yana mai cewa yin la’akari da abin da zai je ya dawo na kare masu yada labarai daga fuskantar tuhumar jami’an tsaro ko shari’o’i a kotuna na neman hakki da kare mutunci.
Ya kara da cewa subul da baka ko fadin abin da ba shi ba na tilasta wa masu isar da sako komawa kafafen yada labarai suna janye kalamansu, karyata kansu, ko bayar da hakuri da alkawarin ba za su sake ba — lamarin da ya ce yana zubar da kima, daraja, da mutuncin marubuta da masu magana a rediyo, talabijin, jaridu, da shafukan sada zumunta.
A karshe, ya bukaci masu gwagwarmaya a fannin sadarwa da su nesanci yada jita-jita, labaran karya, batsa, da duk wani bayani da ba a tantance sahihancinsa ba, yana mai karkarewa da karin maganar nan ta, “Idan kunne ya ji, gangan jiki ya tsira.”

