Hon. Imran Adam Umar Ya Bayyana Goyon Bayansa ga Hon. Aliyu Aminu Garu da Hon. Sa’eed Yusuf Ahmad

Ibrahim Yunusa
Wani dan siyasa kuma mai ruwa da tsaki a Karamar Hukumar Bauchi, Hon. Imran Adam Umar (wanda aka fi sani da Imraanlk), ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana goyon bayansa tare da yaba wa jagorancin Hon. Aliyu Aminu Garu da Hon. Sa’eed Yusuf Ahmad gabanin zabe mai zuwa.
A cikin sanarwar da ya sanya wa hannu, Hon. Imran Adam Umar ya bayyana cewa a ra’ayinsa, jagorancin wakilan biyu abin alfahari ne ga al’ummar Karamar Hukumar Bauchi, duba da abin da ya kira kokarin da suke yi wajen sauke nauyin da aka dora musu.
Ya yi ikirarin cewa wakilcin Hon. Aliyu Aminu Garu da Hon. Sa’eed Yusuf Ahmad ya shafi dukkan sassan Karamar Hukumar Bauchi, ciki har da mazauna cikin gari da na karkara (wajen gari). A cewarsa, babu wata gunduma a fadin karamar hukumar da ba ta amfana da wakilcinsu ba.
Dangane da zabe mai gabatowa, Hon. Imran Adam Umar ya yi kira ga masu zabe a yankin da su yi tunani su kuma sake bai wa shugabannin biyu dama, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ci gaban yankunan Karamar Hukumar Bauchi.
Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da masu ruwa da tsaki, magoya baya, da sauran al’ummar jihar Bauchi ke ci gaba da bayyana ra’ayoyi mabanbanta kan ayyukan wakilan al’umma da kuma makomar siyasar yankin gabanin babban zabe mai zuwa.

