Gobara Ta Shafi Kaburbura A Kalla 11,000 A Makabartar Bauchi

Garba Adamu GwanGwanGwan
Wata gobara da ta tashi a makabartar garin Bauchi a ranar Alhamis ta shafi kaburbura a kalla 11,000, cikin jimillar kaburbura 112,681 da ke yankin.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, daya daga cikin masu kula da makabartar, Musa Muhammad Na’ibi, ya bayyana cewa ana kyautata zaton wutar ta bullo ne ta wata karamar kofa da ke jikin katangar makabartar kafin ta bazu zuwa wasu sassan ciki.
Sai dai kuma, daukin gaggawa da jami’an Hukumar Kwana-Kwana ta Jihar Bauchi suka kai ya taimaka matuka wajen shawo kan lamarin. Jami’an sun yi nasarar kashe wutar tare da dakile yaduwarta zuwa sauran sassan makabartar da gobarar ba ta kai gare su ba.
Kawo yanzu dai, an samu nasarar kammala aikin kashe wutar, yayin da ake ci gaba da duba hanyoyin inganta tsaron katangar makabartar domin kauce wa sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.

