Uncategorized

‘Yan Bindiga Sun Kashe Babban Mataimakin Gwamnan Zamfara a Kaura Namoda

Bashir Ahmad

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun kashe Nasiru Sani Kaura, wani Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, a wani mummunan hari da suka kai a garin Kaura Namoda.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, an harbe marigayin ne a lokacin da maharan suka kai farmaki a yankin Low Cost da ke cikin garin da sanyin safiyar ranar Lahadi. Ganau daga yankin sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kutsa kai cikin unguwar ne daidai lokacin da al’umma ke gabatar da Sallar Asuba, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi. Wannan lamari ya jefa jama’a cikin tsananin firgici, inda kowa ya rika gudun tsira da ransa.

Mutuwar Nasiru Sani Kaura ta jefa al’ummar garin Kaura Namoda da ma fadin Jihar Zamfara cikin matsanancin jimami da alhini. Tuni dai aka gudanar da jana’izar marigayin kamar yadda koyarwar addinin Musulunci ta tanada.

Wannan kisa ya sake bayyana kalubalen tsaro da al’ummar Kaura Namoda da sauran sassan Jihar Zamfara ke ci gaba da fuskanta, inda yankunan ke yawan fuskantar hare-haren ‘yan bindiga. Hakan ya sa mazauna yankin sake jaddada kiransu ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su kara zage damtse tare da daukar kwararan matakai wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Back to top button