Soro United Ta Lashe Gasar Kofin ‘Usman Ya’u Darazo Ganjuwa Unity Cup 2026’

Abdulrahman Bala Katsinawa
An kammala gasar wasan ƙwallon ƙafa ta ‘Usman Ya’u Darazo Ganjuwa Unity Cup 2026’, inda ƙungiyar Soro United ta zama zakara a gasar.
A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun Dr. Lifsa Daniel Daraktan Yaɗa Labarai, na kwamtin yakin neman zaben Arc. Usman Ya’u Darazo, an gudanar da wasannin ne da nufin samar da haɗin kai, zaman lafiya, da ci gaban matasa a Mazaɓar Tarayya ta Darazo da Ganjuwa.
A wajen taron bayar da kyaututtuka, ƙungiyar Soro United da ta zo na ɗaya ta karɓi kofin gasar, lambobin yabo, kyautar kuɗi naira 250,000, buhunan shinkafa guda biyar, da injinan famfon ban-ruwa guda biyu.
Ƙungiyar Soro Warriors, wacce ta zo ta biyu, ta samu lambobin yabo, kyautar naira 100,000, buhunan shinkafa guda uku, da injin famfo guda ɗaya.
An kuma bayar da kyaututtuka ga ‘yan wasa guda uku. Yamal Sadiq Miya ya samu kyautar Gwarzon Ɗan Wasa a gasar, Ukasha Waynee Soro ya samu kyautar Wanda Ya Fi Zura Ƙwallaye, yayin da Hamza Toures Soro ya samu kyautar Gwarzon Mai Tsaron Raga. Kowane ɗaya daga cikinsu ya karɓi kyautar injin famfo guda ɗaya.
Kwamitin shirya gasar ya bayyana cewa shirin na da manufar amfani da wasanni wajen gano matasa masu basira da kuma bunƙasa dangantaka a tsakanin al’umma. Sun kuma miƙa godiya ga dukkan ƙungiyoyi, magoya baya, da shugabannin al’umma da suka bayar da gudunmawa wajen gudanar da gasar.

