Hausa

Rikicin Man Utd: Ƙungiyar Ta Kori Kociyanta Michael Carrick Sakamakon Rashin Kokari

Ibrahim Yunusa

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta sanar da korar mai horaswarta, Michael Carrick, a daidai lokacin da ƙungiyar ke ci gaba da fuskantar matsin lamba wanda ya jefa ta a can ƙasan teburin gasar Premier ta Ingila.

Wannan tsauraran mataki na zuwa ne biyo bayan wata muhimmiyar ganawa da mai mallakar ƙungiyar, Sir Jim Ratcliffe, ya yi da manyan mahukuntan ƙungiyar, wato Omar Berrada da Jason Wilcox a birnin Monaco, inda suka amince da cewa lokaci ya yi da ya kamata a kawo sauyi.

Tun a cikin kwanakin da suka gabata ne dai jita-jita ta cika gari kan makomar Carrick a Old Trafford, yayin da mahukuntan ƙungiyar suka bazama neman sabon kocin da zai ceto ƙungiyar daga halin da take ciki.

Idan ba a manta ba, a baya Manchester United ta yi yunƙurin ƙara ba wa Carrick dama domin gyara kura-kuransa, musamman bayan wani mummunan kashi da suka sha a gida da ci 3-0 a hannun ƙungiyar Bournemouth a ranar 25 ga watan Oktoba, amma al’amura sun ci gaba da taɓarɓarewa.

Back to top button