Focus On BauchiNewsPoliticsVideos
Babu Inda Kaura Zai Je, APC Ta Gama Mutuwa: Salele
A cikin wannan zafafan martani da ya mayar ta hanyar bidiyo, Hon. Hamisu Ahmad Salele, ya yi watsi da shawarar wasu ‘yan APC da ke kiran Gwamna Bala Mohammed da ya daina sukar gwamnatin tarayya ko ya sauya sheka.
Salele ya bayyana cewa kiran Gwamnan ya koma APC “shiririta ce tsagwaronta,” yana mai cewa ai APC ta riga ta gamaargajewa kuma ita ce silar “yunwa da fatara” da ‘yan Najeriya ke ciki. Ya jaddada cewa Gwamna Bala Mohammed shi ne “Dodon APC” kuma shi ne “hasken 2027” da zai ceci Najeriya, don haka babu dalilin da zai sa ya bar PDP ya koma jam’iyyar da ta kasa tabuka komai.
Muhimman batutuwan da ya tabo a martanin:
- Sukar APC: Ya ce APC ta kawo yunwa da talauci, don haka babu mai hankalin da zai bar PDP ya koma cikinta a yanzu.
- Kare Gwamna Bala: Ya ce Gwamna Bala shi ne kadai dan takarar da APC ke tsoro (“Dodon APC”), shi ya sa suke so ya dawo cikinsu don su kashe siyasarsa.
- Rikicin APC: Ya yi tambayar “Ina APC take?” inda ya nuna cewa jam’iyyar tana cikin rikici tsakanin Ganduje da sauran bangarori, don haka ba gida ne na zuwa ba.
- Kiran 2027: Ya tabbatar da cewa Gwamna Bala yana nan daram a PDP kuma shi ne zai yi takara a 2027 don ceto kasar.
Ku kalli cikakken bidiyon domin jin yadda ya yi kaca-kaca da masu kiran Gwamna ya sauya sheka.

