DARAZO ATHLETIC TA ZAMA ZAKARA A GASAR USMAN YA’U DARAZO

Abdulrahman Bala Katsinawa
DARAZO, BAUCHI — Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Darazo Athletic ta lashe gasar Kofin Haɗin Kai ta Usman Ya’u Darazo ta shekarar 2026 (Darazo Unity Cup 2026), wadda aka kammala a mazaɓar tarayya ta Darazo da Ganjuwa a Jihar Bauchi.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Usman Ya’u Darazo, Dr. Lifsa Daniel, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa an shirya gasar ne da nufin ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya, da bunƙasa harkar wasanni a tsakanin matasan mazaɓar.
A ƙarshen fafatawar, Darazo Athletic ta zo ta ɗaya, inda ta samu kofin zakarun gasar, lambobin yabo na zinariya, kyautar kuɗi naira 250,000, buhunan shinkafa biyar, da injinan famfo biyu. A nata ɓangaren, ƙungiyar Darazo United da ta zo ta biyu ta samu lambobin yabo, kyautar kuɗi naira 100,000, buhunan shinkafa uku, da injin famfo guda ɗaya.
Haka kuma, masu shirya gasar sun karrama ‘yan wasa uku da suka yi fice a fannoni daban-daban, inda kowannensu ya samu kyautar injin famfo guda ɗaya. Waɗanda aka karrama sun haɗa da Sadiq Awuwo a matsayin gwarzon ɗan wasa, Kuchi Usman a matsayin wanda ya fi zura ƙwallaye, da kuma Dan Bappah Digiri a matsayin gwarzon mai tsaron raga.
Sanarwar ta ƙara da cewa masu shirya taron na amfani da wasanni a matsayin hanyar gano hazikan matasa da ƙarfafa zumunci a tsakanin al’ummomin yankin. Sun kuma taya ƙungiyoyin da suka yi nasara da sauran ‘yan wasa murna, tare da godiya ga dukkan ƙungiyoyin da suka halarta, magoya baya, da shugabannin al’umma bisa gudummawar da suka bayar wajen gudanar da gasar.

