HausaNews

AN BUƊE GASAR ƘWALLON ƘAFA TA USMAN YA’U DARAZO UNITY CUP 2026

Abdulrahman Bala Katsinawa

A wani gagarumin biki da aka gudanar a garin Darazo, an ƙaddamar da gasar ƙwallon ƙafa ta Usman Ya’u Darazo Unity Cup na shekarar 2026, inda ƙungiyoyin wasanni daban-daban suka fito domin fafatawa da baje kolin basirarsu.

Wannan gasa dai an tsara ta ne a matsayin ɗaya daga cikin muhimman tsare-tsare na bunƙasa harkar wasanni tun daga matakin karkara. Babban burin kafa wannan gasa shi ne ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma, tare da samar wa matasa kyakkyawar damar bayyana ƙwarewarsu da hazakarsu a fagen wasan ƙwallon ƙafa.

Bugu da ƙari, masu shirya wannan wasa sun bayyana cewa gasar wata dama ce ta musamman wajen haɗa kan matasa waɗanda suka fito daga sassa daban-daban na yankin. Ana sa ran wasannin za su taimaka wajen ƙarfafa zumunci, fahimtar juna, da samar da kyakkyawar mu’amala a tsakanin al’umma don wanzar da zaman lafiya da ci gaba.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Kwamitin Kamfen ɗin Arc. Usman Ya’u Darazo, Dr. Daniel Lifsa ya sanya wa hannu, an yi wa dukkan ƙungiyoyin da za su fafata a wannan gasa fatan samun nasara. Sanarwar ta kuma bayyana jinjina da yabawa ga masu shirya gasar, da kuma dukkan waɗanda suka bayar da gudunmawarsu wajen ganin wannan aiki ya tabbata a ƙarƙashin kyakkyawan kudurin nan na “Raya Karkara da Birane”.

Back to top button