Rundunar Sojin Ruwa Ta Rushe Wata Sabuwar Maɓoyar Tsageru A Jihar Cross River

Dini Usman
Rundunar sojin ruwa ta Najeriya, ta bakin dakarun jirgin yaƙinta na ‘NNS VICTORY’, ta yi nasarar gano tare da rushe wata sabuwar maɓoyar da ake zargin ta tsageru ce a ƙauyen gabar ruwa na Ine Ikoridung da ke Jihar Cross River.
Wannan nasarar dai na zuwa ne a matsayin wani ɓangare na ci gaba da kai hare-hare da rundunar ke yi kan tsagerun da ke gudanar da ayyukan assha a yankin Dayspring. An gudanar da wannan sumame ne biyo bayan rahotannin sirri da rundunar ta samu, wanda ya tabbatar da cewa tsagerun sun kaurasa zuwa wannan sabon yankin na gabar ruwa, bayan da matsin lamba da sintirin sojoji ya tarwatsa tsoffin sansanoninsu da ke tsibirin na Dayspring.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar, Laftanar Kwamanda Sulaiman Bala ya fitar, ya bayyana cewa dakarun sojin ruwan sun yi amfani da kwale-kwalen yaƙi inda suka far wa ƙauyen, suka yi wa yankin ƙawanya, tare da gudanar da cikakken bincike a wasu bukkoki da bayanan sirri suka nuna nan ne maɓoyar tsagerun.
Sanarwar ta ƙara da cewa, da ganin tawagar dakarun na tunkaro su, nan take waɗanda ake zargin suka ranta a na zaki. Ko da yake ba a samu damar cafke su ba, dakarun sun samu nasarar ƙwato wasu kayayyaki da suka haɗa da kwanson harsashi guda biyar, rigar kakin sojoji, rigar kakin ‘yan sanda, rigar sanyi ta soji, da kuma hular daji ta sojoji (jungle hat).
Bugu da ƙari, dakarun sun gano wani muhimmin littafin rubutu mai ɗauke da jerin sunayen mayaƙan ƙungiyar da aka kama a baya, da kuma sunayen gidajen gyaran hali inda suke yanke hukuncinsu a halin yanzu.
A ƙoƙarin ganin ba su sake dawowa sun mayar da wurin mafaka ba, dakarun sun banka wuta tare da rushe waɗannan bukkoki baki ɗaya.
A cewar sanarwar, wannan sabon koma-baya da tsagerun suka samu ya biyo bayan irin ruwan wuta da matsin lamba ne da dakarun sojin ruwa ke ci gaba da yi musu, wanda hakan ya hana su sakat tare da tilasta musu yin watsi da asalin maɓoyarsu. Daga ƙarshe, Laftanar Kwamanda Sulaiman Bala ya ba da tabbacin cewa rundunar NNS VICTORY ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da fafatawa da ɓata-garin har sai an tabbatar da an dawo da cikakken tsaro a yankunan ruwan ƙasar nan.

