Focus On BauchiHausaPoliticsVideos

Barauniyar Hanyar Zaben Bauchi: PDP Na Zargin Wata Kwangila Tsakanin APC Da ‘Yan Baranda

A cikin shirin yau na tattaunawa, mun karbi bakuncin Hon. Abubakar Madaki PA, daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP, wanda ya yi tsokaci mai zafi kan batutuwan da ke tashe a Jihar Bauchi.

Madaki PA ya karyata zargin cewa Gwamna Bala Mohammed na shirin sauya sheka zuwa APC, yana mai cewa wannan shaci-fadi ne kawai na wadanda suka kasa tasiri a siyasance. Ya kuma soki lamirin masu ganin akwai rashin adalci daga Hukumar Zabe ta Jihar (BASIEC), yana mai cewa jam’iyyar PDP a shirye take ta fuskanci zabe kuma ba ta da wani tsoro ko shakka.

A cikin wannan hirar da Abdulrahman Bala Katsinawa ya jagoranta, Madaki PA ya yi bayani dalla-dalla kan dalilan da suka sa jam’iyyar PDP ke da karfin gwiwar lashe zabe, duk da zarge-zargen da ake yi wa Gwamnatin Jiha.

Kadan daga cikin abubuwan da ya fada:

  • “Jam’iyyar PDP uwa ce a siyasar Najeriya, kuma babu wani mutum da ya isa ya wargaza ta.”
  • “Gwamna Bala Mohammed ba ya bukatar shiga APC domin yin nasara.”
  • “Duk wani dan takarar da ya fito neman kujera, ya san cewa jam’iyyar PDP tana tare da shi.”

Ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar da ta gudana.

Back to top button