Rikicin PDP A Bauchi: Aminu Shagari Ya Ja Hankalin Gwamnatin Jihar Bauchi.
A cikin wannan tattaunawa ta musamman a Radio LYB, Hon. Aminu Shagari (Sarkin Yakin Kundum) ya warware zare da abawa game da jita-jitar ficewarsa daga jam’iyyar PDP da kuma rikicin da ke faruwa tsakanin masu ruwa da tsaki da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed.
Aminu Shagari ya bayyana cewa shafaffu na kokarin sace zuciyar Gwamna, wajen ingiza shi zuwa ga mantawa da gudumawar da na kusa da shi suka bayar. Ya kuma yi gargadi mai zafi cewa “Idan mutum ya maka rashin adalci step 1, na 2, to kar ka bari a je na 3,” inda ya nuna cewa ba za su ci gaba da zuba ido ana tozarci a jam’iyyar ba.

