HausaNewsPoliticsVideos

Salele

A cikin wata zafafar tattaunawa a shirin “Siyasa da Hali” na Radio LYB, jigon jam’iyyar PDP a jihar Bauchi, Alhaji Hamisu Ahmed Salele, ya yi wasu kalamai masu tada kura inda ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta PDP ba za ta taba amincewa da sabon Shugaban Hukumar EFCC da kuma na INEC da aka nada ba.

A tattaunawar tasa da Abdulrahman Bala Katsinawa, Salele ya yi zargin cewa ana amfani da wadannan hukumomi ne wajen yi wa ‘yan adawa, musamman Gwamna Bala Muhammad na Jihar Bauchi, bita-da-kulli da kuma barazana don a kare muradun siyasar wani bangare.

Ku biyo mu domin jin yadda wannan tattaunawa mai zafi ta kasance tsakanin Hamisu Salele da Abdulrahman Bala Katsinawa.

Back to top button