Hausa

GURBACEWAR AIKIN JARIDA A KAFOFIN SADA ZUMUNTA: KALUBALE GA KWAREWA DA DA’AR AIKI

Aliyu Zakari

Idan aka yi duba na tsanaki kan yadda ake tafiyar da al’amura a kafofin sada zumunta, za a fahimci cewa babu wata sana’a da ta yi kaurin suna wajen shigarta ta barauniyar hanya (sojan gona) kamar aikin jarida. Wannan gurbacewa ta samo asali ne saboda rashin tsari da sakaci wajen dakile illolin da ke tattare da aikin, musamman daga bangaren masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai.

Abin takaici ne yadda shafukan sada zumunta, musamman Facebook, suka koma dandalin yada karairayi, cin zarafi, batanci, da rashin girmama na gaba, ciki har da malaman addini. A yau, mallakar wayar salula (smart phone) da ‘data’ kadai ya zama ma’aunin zama ‘dan jarida’ ga wasu. Wannan yanayi ya samu gindin zama ne saboda yadda wasu ‘yan siyasa ke rungumar irin wadannan matasa don isar da sakonninsu, masu kyau da marasa kyau, ba tare da tace su ba ko la’akari da ka’idojin aiki.

Babban abin tambaya a nan shi ne: Me ya sa ‘yan siyasa ba sa daukar nauyin wadannan matasa zuwa makarantu don su koyi aikin jarida a hukumance? Amsar a fili take; son zuciya da biyan bukata ta gaggawa shi ne gabansu, yayin da suke disashe makomar matasan da ke yi musu hidima, wadanda galibi ba sa gane kurakuran su sai lokaci ya kure.

Sako zuwa ga masu sha’awar aikin jarida: Kwarewa ita ce gishirin aiki. Yana da kyau ku nemi ilimin aikin jarida a hukumance har ku mallaki takardar shaida. Wannan ba wai zai halatta muku hanyar cin abinci kadai ba ne, zai sa ku yi alfahari da kanku, ku kuma samu daukaka mai dorewa a nan gaba. Rashin ilimi a wannan fage shi ne yake janyo wa da yawa fadawa komar hukuma da nadama marar amfani.

Zuwa ga ‘yan siyasa: Ku daina amfani da matasa a matsayin ‘yan barandan banga-siyasa a kafofin yanar gizo. Ku taimaka musu wajen samun ilimi da kwarewa. Hakan zai inganta manufofinku, ya kuma gina al’umma mai nagarta.

A karshe, ina kira da babbar murya cewa mu ji tsoron Allah a duk abin da za mu rubuta ko yadawa. Mu tuna cewa duk abin da mutum ya shuka shi zai girba, kuma akwai ranar hisabi a gaban Mahalicci.

Aliyu Zakari

aliyuzakari320@gmail.com

09125818181

Back to top button