Majalisar Shura Ta Ja Hankalin Al’umma Kan Illolin Fita Zanga-Zanga
Daga Abdurrahman Bala Katsinawa
Majalisar Shura ta Al’ummar Musulmin Jihar Bauchi, ‘Bauchi State Muslim Parliament’, ta barrantar da kanta ta kowani janibi cikin matakan da wasu suka dauka na gudanar da zanaga-zanga game da halin tabarbarewar rayuwa cikin tarayyar Nigeria, kana ta yi kira ta musamman ga masu shiga zanga-zanga kan illolin da hakan ka iya jawowa ga zaman lafiyar kasa.
Shugaban Majalisar, Mal. Yusuf Abdullahi Jahun shi ya bayyana matsayin Majalisar a ganawar sa da ‘yan jarida a garin Bauchi, in da ya bayyana cewa bisa al’adarta duk lokacin da wani abu ya taso, Majalisar ta kan yi zama ta tattauna, ta nazarci abin sosai, ta zurfafa bincike matuka.
Ya ce babu shakka akwai tsanani da matsatsi na rayuwa, kuma Majalisar Shura ta yarda ta gamsu da akwai wannan, amma matsatsi da tsanani lokacin da suka faru, shugabanni jagororin jama’a, abin da fassarar shugabanci ya ke kai shi ne a samar da saukin rayuwa ga wadanda ake shugabanta, da kyautata rayuwar wadanda ake shugabanta, wannan shine ruhi na shugabanci.
Mal. Abdullahi Yusuf Jahun ya kara da cewa, “nazari ga bangaren neman hakki ko sauki ta fuskar zanga-zanga, shi ma mun nazarce shi nazari mai kyau. Ba wannan kasa ta mu ba, kasashe da suke makwabtanmu, kasashe da suke ‘yan uwanmu a Afurka, kasashe da suke sassan duniya daban-daban, an yi amfani da irin wannan hanyar da sunan neman hakki, ko sassauci amma mun ga abinda irin wannan abu ya haifar”.
A cewar sa, “ganin wannan, sai muka tsaya a matsaya cewa wannan hanyar, Majalisar Shura bata tare da ita, a matsayin hanya ta neman sassauci ko sauki, ko neman mafita ga halin da ake ciki, saboda abin da hakan ya haifar a kasashe da suka gabaci wannan kasa tamu da suka yi wannan abu da abin da hakan ya jefa su ciki. An wayi gari, abin da aka rena din aka rasa shi kwata-kwata, an ma rasa komi, an kuma rusa kasashe, an wargaza kasashe da irin wannan salo, ko wannan hanyar, wanda farkonsa ya kan soma ne da zanga-zanga don neman hakki. A saboda haka muna fatan suma su kalli abin da muka kalla, cewa wannan ba hanya ce mai bullawa ba”.
A bangare shugabanci kuwa, Majalisar Shura ta bakin shugabanta ta mika shawara da jan hankali da cewa, “a sashen shugabanci da jagoranci da sukan bar al’amurra su lalace, su kai ga irin wannnan matsaya na tasanani da takura wa ‘yan kasa, har su nema wa kansu mafita da sassauci, da sauki ta hanyar da ba ta dace ba, lallai su dawo su koma kan kai’dar da shugabanci ya shimfida. Shugabanci shi ne ba da kaykkyawar rayuwa ga wanda ake shugabanta; kiyaye ma wanda ake shugabanta maslahohi ta rayuarsa duniya da lahirarsa; da maslahohi ta rayuwarsa ta yau da kullum”.
Ganin yanda al’amurra suka ta’azzara da kuma ko wannan sako na zai cimma shugabanni, Mal. Yusuf Abdullahi Jahun ya fayyace cewa, Majalisar Shura ta rubuta takarda zuwa ga shugabanni kunshe da wadannan shawarwari ta kafar da za ta cimma masu, da fatan shugabannin za su dawao da kasara daga yanayi da ya jefa wannan kasa cikin halin da ta ke ciki, zuwa ga yanai mai kyau.
Ya kammala da cewa, “abin da duk ya sabbabar da yanayi maras kyau din, muna fata shugabanni za su nazarce shi, su nakalce shi, su gyara, su kuma kyautata. Musamman abin da wasu manazarta suke ambata maganar janye subsidy, ma’ana tallafi da akay yi wa mai, da sauran wasu al’amurra na rayuwar al’ummar kasa shi ya jefa kasa cikin fatar da talauci, inda ya zamo abinci na gagaran dan kasa. Muna fata za su dawo da wannan subsidy din, kuma za su dawo da dukkan ahanyoyi na gudanarwa wadanda za su inganta su kyautata rayuwar al’ummar kasa.”

