Hausa

Masu Sauraro Na Maraba Da Radio LYB

  Daga: Khadija M. Bello

‘Yan watanni da kaddamar da tashar Radio LYB mai watsa shirye-shirye a yanar gizo don fara gwada kamun ludayin aiki, yanzu sannu a hankali wannan kafar ta na kara samun masu sauraro da ke bibiyen shirye-shirye masu kayatarwa cikin harsuna 3 da tashar ke gabatar da wadannan shirye-shirye, wato cikin Hausa, Turanci da kuma Larabci don masu sauraro a fadin duniya.

Shi dai shirin gwaji na radiyon ya fara ne a farkon watan Janairu har zuwa watan Fabreru na wannan shekara ta 2024, amma kafin ka ce kwabo da shiga watan Maris, wanda a lokacin ne al’ummar musulmi ta dau azumin watan Ramadan, sai yawan masu sauraron wannan kafar sadarwa ya karu daga ‘yan gwashar zuwa kusan miliyan 3 cikin lokaci kankani., musamman makon farko na watan Ramadan.

Wannan karuwa da kafar ta samu na masu sauraro ba zai rasa nasaba da jerin shirye-shirye na Tafsir da sauran darussa na fadakarwa da ilmantarwa game da azumi da abubuwan da ke da alaka na kut-da kut da watan Ramadan ba, lura da muhimmanci da al’ummar musulmi ke bayarwa ga wannan wata mai cike da albarka da alheri.

Yanzu haka dai akwai kan wannan kafa ta Radio LYB jerin shirye-shirye na Tafsir daga Masallatai da dama, wadanda wasu manyan Malaman addini fitattu ke gabatarwa, da suka hada da Imam Muhammad Yusuf Adam, Imam Mahmoud Tanko Aliyu Zungur, Sheikh Muhammad Kabir Yakubu Arabi, Sheikh Mahmoud Ibrahim Shira, Malam Sa’idu Hamid Bello, Professor Muhammad Safiyyu Abdulkadir Jahun, Imam Mu’azu Idris Guyaba, Imam Saddam Abubakar, Imam Yusuf Ibrahim Bauchi, Sheikh Muhammad Attahiru Bakoji, kana da wasu Tafsiran da aka tanada cikin sauti na wasu Malaman da suka rigamu gidan gaskiya, kamar Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam da kuma Sheikh Abdurrahman Ajlan na kasar Saudiyya wanda ya gabatar a Masallacin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi.

Duk wadannan jerin Tafsirai, dadi ne kan wasu shirye-shirye na addini da karin Malamai ke gabatarwa kamar su Professor Salisu Shehu (Walin Tafawa Balewa), da Ustaz Umar Muhammad, kana da wani shiri na musamman da ke maida hankali kan rayuwar al’umma ta yau da kullum cikin watan Ramadan, sannan da karin filaye na tallace-tallace da isar da fatan alheri ga al’umma da sauran abokan hulda.

Da na nemi jin ra’ayi masu sauraro a garin Bauchi, na yi kicibis da wadanda suka bayyana farin ciki da gamsuwa game da shirye-shiryen wannnan sabuwar kafa ta radio mai watsa shirye-shirye a yanar gizo, musamman game da abin da ya shafi kyan sauti da kuma irin Malaman da ke da kwarewa wajen gabatar da darussa na Tafsir.

Ibrahim Mohammed wani mai sauraro ne da ya ce shi Tafsirin Jalalaini kadai ke saurara kan wannan kafar, domin abu ne da aka rasa bisa tsarin karatun zaure da al’umma ta saba, amma sai ga shi wannan radio na kawo guda 3 cikin irin wannan tsarin gabatar da Tafsiri.

Shi kuwa Mallam Salisu Gwabba ganin cewa tashar na watsa shirye-shirye ne tsawon sa’o’i 24 a rana, ya ce “yanzu hankali kwance na ke sauraron Tafsir tare da samun gamsuwa tsawon dare lokacin da na ke gudanar da wasu ayyuka.”

Wani bincike da na gudanar ya nuna cewa a lokacin da wannan kafa ta Radio LYB ke kara samun masu sauraro da tagwammashi, akwai wani yunkuri na kara inganta shirye-shiryen kafar bisa tsari na bincike mai gamsarwa a mahanga ta ‘yan Nigeria don dacewa da bukatun karin ilimi da fadakarwa ga masu sauraro a duniya.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button