Focus On BauchiHausaNewsVideos

Ko kun San Tarihin Hawan Sallah A Masarautar Bauchi?

A lokaci na hidimar Eid -El Fitr (sallah) da biki na raya tarihi da al’adu managarta a masarautun karkashin Daular Usman Dan Fodio, Radio LYB Online, ya samu tattaunawa ta musamman tare da Alhaji Ado Danrimi Garba (Wakilin Tarihin Masarautar Bauchi Na Farko), kana Darektan Cibiyar Tarhi, Bincike da Adanar Kayan Tarhi ta Masarautar Bauchi.

Cikin wannan tattaunawa a daidai lokacin da al’ummar musulmi ke farin cikin ganin wannan yanayi na hidimar sallah da alkinta al’ada da tarihi a shekarar hijira 1445, daidai da shekara bta 2024, masanin tarihin kan al’amurran Daular Usmaniyya, ya yi dogon sharhi kan bangarori, da sassa, kazalika da muhimman abubuwa da suka shafi canjin zamani da karin habaka cikin harkokin masarautu.

Daukar misali da masarautar Bauchi, wanda ya ce ta yi fice, kana jagora ce cikin karfafa ginshinkin kafuwar wannan daula ta Usman Dan Fodio, Wakilin Tarhin Masautar Bauchi, ya gina sharhi da misalai, kana da daldale bayani kan yanda tarihi ya ginu game da batun bikin sallah a masarauta.

Me alakar fadojin Sarakunan kasar Daular Usmaniyya da hawan sallah; yaushe aka fara wannan lamari a masarautar Bauchi; ta ina wannan al’adar ke taimakawa wajen bunkasa tarihi da karfafa dorewar al’adun masarautu; ina bambanci tsakanin hawan sallah da hawan bariki; ta ina wannan al’ada ta yi kama da juna a duk masarautun jihar Bauchi, ina kuma suka sha bamban; sannan ta ina karin yawan Hakimai ke shafar gudanar da raya wannan al’ada cikin nasara, ko akasi?

A biyo shirin sannu a hankali don sauraron gabobin wadannan bayanai kan tambayoyi daki-daki a jere ta wannan shafi na Radio LYB.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button