Focus On BauchiHausa

Jerin Hakimai Masu Hawan Sallah A Masarautar Bauchi

Rahoto Na Musamman: Dalhat Hamid Bello

Wannan Laraba ce ke kasancewa 1 ga watan Shawwal, 1445, kamar yanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji (Dr.) Muhammad Sa’ad Abubakar CFR mni ya sanar a sakonsa na tunatar da al’ummar musulmin Nigeria cikan kwanakin watan Ramadan 30 a wannan Talata, don kammala azumin bana cikin falala da kyautatawar Allah, Madaukakin Sarki.

A duk kewayowar shekara dab bayan kammala azumin watan Ramadan, lokaci ne na hidimar Eid -El Fitr (karamar sallah) da biki na raya tarihi da al’adu managarta a masarautun karkashin Daular Usman Dan Fodio a tarayyar Nigeria. Dukkan masarautu karkashin wannan daula a ranar Sallah, da ma wasu kwanaki bayan Sallah kan shirya bukukuwa na murnar wannan hidima, don raya tarihin kasashen sarautunsu, tare da kara inganta abubuwan da al’ada da tarihi suka bar gajiya wa al’umma ta baya cikin gudanar da wadannan al’amurra.

Cikin zantawar sa da Radio LYB Online, Alhaji Ado Danrimi Garba (Wakilin Tarihin Masarautar Bauchi Na Farko), kana Darektan Cibiyar Tarhi, Bincike da Adanar Kayan Tarhi ta Masarautar Bauchi, ya fadi cewa  bijiro da irin wannan biki na Sallah cikin harkokin masautun daular Usman Dan Fodio “na da muhalli a bigire na addini”, in da ya kara da cewa, ko lura da yanda Mai Martaba Sarkin Bauchi ke gudanar da akasarin ayyukansa na sarauta da hidimar masarauta, “koyi ya ke da sunnah ta Manzon Allah”, musamman wajen sanya sutura, gudanar da ibada, da sauran mu’amaloli na tsakanin mai sarauta da talakawa.

Cikin wannan tattaunawa a daidai lokacin da al’ummar musulmi ke farin cikin ganin wannan yanayi na hidimar sallah da alkinta al’ada da tarihi a shekarar hijira 1445, daidai da shekara ta 2024, masanin tarihin kan al’amurran Daular Usmaniyya, ya yi dogon sharhi kan bangarori, da sassa, kazalika da muhimman abubuwa da suka shafi canjin zamani, bunkasa, habaka da kuma fadada cikin harkokin masarautu.

Daukar misali da masarautar Bauchi, wanda ya ce ta yi fice, kana jagora ce cikin karfafa ginshinkin kafuwar wannan daula ta Usman Dan Fodio, Wakilin Tarhin Masautar Bauchi, ya gina sharhi da misalai, kana da daldale bayani kan yanda tarihi ya ginu game da batun bikin sallah a masarauta, ka’idoji da masarauta da gindaya, sannan da kokari na masu kula da harkokin sarauta ganin wadannan abubuwa ba a bar su kara zube son zuciya da rashin kishin al’ada da sarauta sun sababta ruguza su ba.

Me alakar fadojin Sarakunan kasar Daular Usmaniyya da Hawan Sallah; yaushe aka fara wannan lamari a masarautar Bauchi; ta ina wannan al’adar ke taimakawa wajen bunkasa tarihi da karfafa dorewar al’adun masarautu; ina bambanci tsakanin Hawan Sallah da Hawan Bariki; ta ina wannan al’ada ta yi kama da juna a duk masarautun jihar Bauchi, ina kuma suka sha bamban; sannan ta ina karin yawan Hakimai ke shafar gudanar da raya wannan al’ada cikin nasara, ko akasi?

Cikakkiyar wannan tattaunawar ta na adane a sassanmu na Radio mai dauke da murya, da kuma YouTube mai motsi. A biyo shirin sannu a hankali don sauraron gabobin wadannan bayanai kan tambayoyi daki-daki a jere ta wannan shafi na Radio LYB.

A halin da ake ciki don tabbatar da tsabtatacciyar hidimar Sallah a masarautar Bauchi, Majalisar Fadar Masarautar ta kafa kwamiti na musamman da ya kimtsa tsare-tsare, da tanade-tanade, kazalika da ka’idoji na fita Hawan Sallah, da Hawan Bariki, inda aka zayyana jerin sunaye na Hakimai masu wannan hawa, da hanyoyi da mahaya da tawagar Mai Martaba Sarki za su tafi kai, sannan da abubuwan da za a gudanar a Fadar Sarki da kuma Gidan Gwamnatin jihar Bauchi.

Wata takarda mai kunshe da dukkan wadannan bayanai daga ofishin Jami’in Yada Labarai na Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alh. Babaginda Hassan Jahun, ta bayyana cewa Kwamitin tsara Hawan Sallah ya kasance karkashin Dr. Baba Muhammad Gidado (Madakin Bauchi), Hakimin kasar Ganjuwa, sannan  kayyadaddun Hakimai masu Hawan Sallah su (55) Mai Martaba Sarki ya amince da su yi hawa, wadanda suke a jere kamar haka:

 1. Dr. Baba Muhammad Gidado (Madakin Bauchi)
 2. Alh. Aliyu Yakubu Lame (Sarkin Yakin Bauchi)
 3. Alh. Umar Adamu Waziri (Katukan Bauchi)
 4. Dr. Mohammed Ahmed Shehu (Dan Amanan Bauchi)
 5. Alh. Nasiru Musa Sudani (Madahun Bauchi)
 6. Alh. Muhammad Yakubu III (Sarkin Yamman Bauchi)
 7. Nuru Adamu Jumba (Chiroman Bauchi)
 8. Alh. Tirmisiyu T. Adegoke (Oba Yuruba)
 9. Chief Igwe Jude Umezika (Eze Ndi Igbo)
 10. Alh. Abubakar Sulaiman B. (Ganuwan Bauchi)
 11. Alh. Sadiq Musa Liman (Sarkin Dawakin Bauchi)
 12. Dr. A. G. Hassan (Uban Garin Bauchi)
 13. Hon. Aliyu Aminu Garu (Sarkin Alhazan Bauchi)
 14. Alh. Shehu Adamu Jumba (Danlawan Bauchi)
 15. Alh. Bala Suleiman Adamu (Dangaladiman Bauchi)
 16. Alh. Yakubu Sani (Sardaunan Bauchi)
 17. Alh. Garba Sambo (Yariman Bauchi)
 18. Mal. Hussaini Abubakar Othman (Dan Jikan Bauchi)
 19. Alh. Muhammad Abba (Darman Bauchi)
 20. Alh. Labaran M. Makera (Dan Sararin Bauchi)
 21. Alh. Yakubu Ahmed Kari (Dattuwa Mangan Bauchi)
 22. Alh. Yakubu G. Umar (Dan Darman Bauchi)
 23. Alh. Muhammad Hamza (Sarkin Gabas Bauchi)
 24. Alh. Ahmed Yakubu Wanka (Sarkin Dawaki Mai Tuta)
 25. Sen. Abubakar Maikafi (Danmadamin Bauchi)
 26. Alh. Ahmed Adamu Ambi (Majidadin Bauchi)
 27. Alh. Umaru Dahiru (Baraden Bauchi)
 28. Alh. Bala Attahiru III (Ajiyan Bauchi)
 29. Alh. Suleiman Muhammad (Barden Bauchi)
 30. Prof. Yusuf Hassan Bashir (Tafidan Bauchi)
 31. Sen. Adamu Ibrahim Gumba (Kuyambanan Bauchi)
 32. Alh. Jibrin Hussaini Jibo (Dan Saran Bauchi)
 33. Alh. Sani Ahmed Abubakar (Chika Sararin Bauchi)
 34. Mal. Sharif Nasir Bello (Sarkin Sharifan Bauchi)
 35. Alh. Babayo Ibrahim Bababa (Sarkin Darazo)
 36. Hon. Danlami Ahmed Kawule (Barden Arewan Bauchi)
 37. Dr. Hayatu Mustapha Bello (Barden Kudun Bauchi)
 38. Alh. Abdullahi Abba (Sarakin Bauchi)
 39. Alh. Abdullahi Hussaini (Sarkin Tandun Bauchi)
 40. Alh. Mijinyawa Hassan (Falakin Bauchi)
 41. Abdullahi Abba Jibrin (Gandun Bauchi)
 42. Alh. Muhammadu Da (Iyan Bauchi)
 43. Alh. Muhammad Tukur Mato (Sarkin Kasidun Bauchi)
 44. Alh. Ibrahim Y. M. Baba (Sarkin Yelwan Duguri)
 45. Alh. Musa A. Fateh Jahun (Wakilin Gonan Bauchi)
 46. Alh. Garba Muhammad Noma (Jarman Bauchi)
 47. Alh. Abdullahi Umar (Mai Bornon Bauchi)
 48. Alh. Abdulkadir Mahmud (Wakilin Raya Kasar Bauchi)
 49. Alh. Adamu Mohammed (Sarkin Duguri)
 50. Alh. Abubakar Musa Saleh (Sarkin Bula)
 51. Alh. Sadiq Ladan Abdullahi (Sarkin Itatuwan Bauchi)
 52. Sen. Halliru Dauda Jika (Dokajin Bauchi)
 53. Alh. Uba Ahmed Kari (Wazirin Bauchi)
 54. Alh. Lawan Muhammad Kirfi (Wamban Bauchi)
 55. Surv. Ibrahim Sa’idu Jahun (Galadiman Bauchi)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button