Hausa

Gwamnatin Jihar Kebbi  Ta Mika Tallafin Karatu Ga Dalibai

Daga Khadijah M. Bello

A wani yunkuri na bunkasa harkar ilimi a jihar Kebbi, Gwamnan jihar, Alh. Nasir Idris  ya mika tallafin kudi na Naira miliyan 309.5 (Miliyan Dari Uku da Tara, da Dubu Dari Biyar) ga ɗaliban jihar da ke karatu a ƙasashen waje don ci gaba da karatun su ba tare da wata tangarda ba.

Cikin umurnin da ya bayar na biyan wanna kudi, bayani na nuna cewa kudin zai shiga hanun ‘yan asalin jihar ta Kebbi da ke karatu a kasashen Indiya da masar su 86 ta hanun jami’ai masu kula da fannin ilimi a jihar.

Kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Kebbi,  Alh. Isah Abubakar Tunga shi ya ba da cikakken bayanin haka lokacin da yake ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi.

Kwamishina ya ce, Gwamna Nasir Idris ya biya kuɗin tallafin karatu na ƙasashen waje ga ‘yan asalin jihar Kebbi da ke karatu a Indiya da Masar su 109 da ke karatu a cibiyoyin ilimi daban-daban kan wasu muhimman kwasakwasai da jihar ke bukatan su a wadannan kasashe na waje.

Kwamishinan na ilimi ya kara da cewa akwai sauran ɗaliban da ke karatu a ksashen waje  guda 50 wadanda nan ba da jimawa ba za a biya nasu kuɗaɗen, a dan cikin ƙanƙanin lokaci mai zuwa da yardar Allah.

Wannan yunkuri na Gwamnan jihar Kebbi ya zo ne biyo bayan  biyan duk ɗaliban da suka cancanci samun tallafin karatu a jihar wadanda ke karatu a manyan makarantu 36 a faɗin ƙasar tun cikin watan Fabrairu, na wannan shekara ta 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button